Fiqhul-Muyassar: Fiqhu A Saukake Fassarar Hausa


2.7 par AcademiaApps
Aug 15, 2020

À propos de Fiqhul-Muyassar: Fiqhu A Saukake Fassarar Hausa

Fiqhul-Muyassar: Littafin Fiqhu A Saukake Fassarar Hausa.

Fiqhu A Sauqaqe

Don Allah idan har kaji dadin wannnan application mai suna Fiqhul-Muyassar: Fikhu A Saukake Fassarar Hausa a taimaka a yi sharing ta facebook, whatsapp, twitter, instagram da dai sauran social media domin sauran yan uwa musulmi su ma suyi downloading su amfana.

Kada kuma a manta ayi rating na wannnan application five star.

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah mabuwayi, tsarkkaken sarki. Tsira da aminci su tabbata ga fiyyayyan halitta Annabin karshe Annabi Muhammad SAW, da alayensa da sahabban da kuma wadanda suka bi su da kyautatawa har ranar sakamako.

Wannan littafin mai suna Fikhul Muyyasar ya kunshi ibada da mua’amala a shari’ar musulunci ta hanya mai sauki. Ya fara tun daga tsarki har zuwa zamantakewa tsakanin al’ummah. Allah ya sa wa wannan aiki albarka, ya kuma sa iklasi a ciki, amin.

Ibrahim Abdullahi.

Minna, Nigeria.

GABATARWA MAWALLAFI.

Matsayin fikhu da girmansa a cikin zukatan musulmi.

Muhammancin matsayin fiqhu.

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah shi kadai, tsira da aminci su tabbata ga Annabin da babu wani Annabi bayan shi, lalle yana daga cikin zance mai amfani mu kara tabbatar da cewa ilimin fikhu yana daga cikin mafi matsayin ilimomi addinin musulunci, da haka ne za mu gane cewa fiqhu tushe ne da ya kasance musulmi yake auna aikin shi da shi, game da abin da aka halasta ko aka haramta, ingantacce ko batacce, kuma musulmai gaba daya suna kwadayi wajan neman sani halas da haram, ingantacce ya shafi alakar su da Allah ko bauta masa, na kusa ko na nesa, makiyi ko aboki, shugaba ko wanda ake shugabanta, musulmi ko wanda ba musulmi

ba, kuma babu wata hanya ta sanin haka sai ta ilimin fikhu.

Wanda ke bincike game da hukuncin Allah akan bayi gaba daya, na umurni ko na zabi ko kuma wanda aka tilasta.

Lokacin da ilimin fikhu ya kasance daban daga sauran ilimomi, ya ta fadada ta hanyar anfani da shi, kuma muhimmancin shi ya ta girmama, da haka ya hada hanyoyin ci gaba da bunkasa kuma ya tattara abubuwan more rayuwa, sa’anan ya tabbatta shi mai tafiya da zamani ne, da haka ya hada hanyoyin ci gaba da bunkasa, sa’annan bunkasar ta sa ta tsaya ko ta kusa tsayawa, kodai da gangan ko kuma domin lalle shi ya nisanci barin dogaro ko riko da wani bangare na rayuwa (kamar yadda wasu suke ganin ya takaitune da tsarki da sallah, alhalin bah aka ba ne), domin neman sauyin na daular musulunci wanda aka sanya shi batare ba da al’adunsu da dabi’unsuba,

tare kuma da sadar da shi akan abin mamaki da haskaka sai ya bata musu rayuwa, kuma ya sanya musu mishikiloli kuma da kwadayi don amfani da wannan ilimin ba tare da an yi ba, watsi da shi ba domin shi ne ilimin mai girma ba, sai don karfin ginshikin shi da kuma hukunce-hukuncen da ya ginu akai, wanda ba ya gushewa akan tubalin shi daram a tsawo lokaci mai tsawa.

Hakika Allah madaukakin sarki ya yi umurni game da wannan al’umma da su inganta fannin sa kuma su karantar da yadda za’a yi amfani da shi a karance da kuma a aikace.

Sai muka ga mafi yawan kungiyoyin musulunci suna ta kokarin komawa zuwa ga Shari’ar Allah, har ya zo ya kasance babu wata kungiya da zata yi amfani da wani tsari sai dai ‘yan kadan wadanda suke ganin rayuwarta hade yake da rayuwarsa, kuma karuwar arzikinta hade ya da wanzuwarsa. Amma dai

Allah zai bayyanar da addinin shi koda mushirikai sun ki.

Sai, ai yaushe aka fara amfani da fikhu? Menene sababin amfani da shi? Da me fikihu ya kebanta da me kuma ya yi fice? Meke zama wajibi akan musulmi wajan kokarin aiki da shi? Da bayanin kamar haka.

An fara amfani da fikhu ne a sannu-sannu a zamanin Annabi SAW da kuma lokacin sahabbai, kuma sababin amfani da shi tare da bayyana shi a farkon lokaci a tsakanin sahabbai shi ne, matsananciyar bukatar da mutane suke da ita na sanin hukunce-hukuncen sababbin wadanda suke ta aukuwa, da haka ne bukatuwar fikhu ta mamaye kowanne zamani, domin tsara alakar zaman-takewar mutane da kuma jawo abubuwan gyara da kuma kore abubuwa cutarwa, da barin barna kai tsaye tare da matsayin ilimin fikhu da abin da yake da shi.

Quoi de neuf dans la dernière version 2.7

Last updated on Nov 14, 2020
This Update includes bug fixes and improvements

Informations Application supplémentaires

Dernière version

2.7

Telechargé par

قائد النمور

Nécessite Android

Android 4.1+

Voir plus

Use APKPure App

Get Fiqhul-Muyassar: Fiqhu A Saukake Fassarar Hausa old version APK for Android

Téléchargement

Use APKPure App

Get Fiqhul-Muyassar: Fiqhu A Saukake Fassarar Hausa old version APK for Android

Téléchargement

Alternative à Fiqhul-Muyassar: Fiqhu A Saukake Fassarar Hausa

Obtenir plus de AcademiaApps

Découvrir